Dalilin da ya hana sojojin Najeriya murkushe Boko Haram – Kwamanda

Dalilin da ya hana sojojin Najeriya murkushe Boko Haram – Kwamanda

Babban kalubalen da ke kawo cikas ga rundunar sojin Najeriya wajen murkushe kungiyar yan ta’addan Boko Haram shine rashin helikwafta na sojoji, inji mutumin da ke jagorantar ayyukan rundunar soji akan kungiyar yan ta’addan.

Olusegun Adeniyi, wanda ya kasance kwamandan rundunar soji na Operation Lafiya Dole, ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kwamitin majalisar dokokin tarayya akan harkokin rundunar soji a ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoba.

Mista Adeniyi, wanda ya kasance Manjo Janar ya karbi ragamar rundunar wacce ke yaki da ta’addaci kimanin watanni biyu da suka gabata.

Tawagar na karkashin jagorancin shugaban kwamitin, Sanata Ali Ndume, wanda ya ce sun kai ziyarar ce ta kwanaki biyu, domin su gane wa idon su halin da ake ciki.

Duk da cewa Boko Haram sun kashe dubban jama’a a shekarun baya, Adeniyi ya jajirce cewa Boko Haram ba wani marga-margan karfi gare su ba.

“Yan Boko Haram ba wani karfi ke gare su ba sosai. Boko Haram ba su ma iya jure minti 15 ana musayar wuta da su. Taron yuyuyu ne.

“Saboda na yi yaki da su gaba-da-gaba a Marte, Delta da Gubio, a lokacin da na mataimakin kwamanda da kuma lokacin da yanzu na ke kwamanda.”

Daga nan sai ya ce wa sanatocin, “ina rokon ku idan kun je Abuja, ku sanar cewa Boko Haram fa ba wata tsiya ba ce, ‘yan samame ne kawai.”

KU KARANTA KUMA: Duka tatsuniyar gizo da koki ce: Bidiyon da ke yawo ba na kamun auren Sadiya Farouq da Buhari bane

Adeniyi ya yi magana mai tsawo a kan muhimmancin sojojin kasa su samu helikwafta na su na kan su. Ba wai a rika dogara da jiragen yakin sojojin sama ba.

“Sojojin sama na kokari matuka, toh amma fa akwai tazara daga inda suke," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel