Zaben Shugaban kasa: CUPP na zargin akwai munakisa da aka shiryawa karar Atiku a Kotun koli

Zaben Shugaban kasa: CUPP na zargin akwai munakisa da aka shiryawa karar Atiku a Kotun koli

Kungiyar gamayyar jam’iyyun siyasa ta CUPP na zargin gwamnatin tarayyar Najeriya da matsawa Alkalin-alkalai, Jastis Tanko Muhammad a kan ya amshi sunayen wadansu mutane a matsayin wadanda suka nan lokacin da kotun zabe ta yi hukuncinta.

A cikin wata hira da kakakin kungiyar yayi da manema labarai jiya Alhamis a Abuja, Ikenga Imo Ugochinyere ya ce ko kadan kungiyarsu ba zata aminta da wannan yinkurin ba, saboda ana kokarin yiwa karar Atiku Abubakar zagon kasa ne.

KU KARANTA:Gwamnatin Buhari ko gandun barayi, inji jam’iyyar PDP

Atiku Abubakar dai shi ne dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasan 2019, inda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben.

Atiku ya garzaya zuwa Kotun kolin ne kasancewar kotun daukaka kara tayi watsi da kararsa inda yake kalubalantar nasar Buhari a zaben da ya gabata.

Ugochinyere a cikin jawabinsa ya ce babu yadda za ayi a ce a bar gwamnati mai ci ta yiwa Atiku abinda ta ga dama dangane da wannan shari’ar.

Ikenga ya ce: “Muna da masaniyar cewa gwamnatin APC mai ci a yanzu na amfani da karfinta na mulkin domin ta tursasa Jastis Tanko ya amshi sunayen wadansu mutane a matsayin wadanda suka halarci kotun zaben.

“Akwai matsala babba kasancewar Kotun kolin ma ba ta tsira ba daga irin wadannan abubuwa. Ba zamu taba yin shiru ba mu zuba ido muna kallo a aikata rashin gaskiya, dole mu yi magana, hakan ne ya sanya muke gargadin Kotun koli da kada ta kuskura tayi wani abinda ya saba ka’ida ko yaya na.” Inji kakakin.

https://guardian.ng/news/cupp-alleges-plot-against-atikus-appeal-at-supreme-court/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel