Buhari ya taya firam ministan Habasha murnan samu kyautar Nobel

Buhari ya taya firam ministan Habasha murnan samu kyautar Nobel

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Firam ministan kasar Habasha (Ethiopia), Abiy Ahmed, murnan samun kyautar Nobel na zaman lafiya.

A yau, Kwamitin Nobel ta Royal Swedish Academy ta baiwa Abiy Ahmed lambar yabon Nobel sakamakon sulhun da yayi tsakanin kasarsa da kasar Eriteriya bayan shekaru 20 da aka kulla gaba.

Shugaba Buhari yace: "Ina taya Firam minista Abiy Ahmed, wanda aka alanta yau matsayin zakaran lambar yabon Nobel na zaman lafiya kan sulhunta gaban shekaru 20 da yayi tsakani kasar Habasha da Eriteriya.

"Wannan alama ce mai kyau ga hanyoyin samar da zaman lafiya tsakanin kasashen Afrika da na ketare."

"Na yi imanin cewa cigabar Afrika na rataye kan zaman lafiya tsakaninmu da kuma kokarin gwamnatoci da al'ummarsu. Wajibi ne mu hada kai da juna domin samar da zaman lafiya a fadin nahiyar."

KU KARANTA: Shikenan, kotu ta kwace kujerar Sanata Dino Melaye

Kyautar Nobel na daga cikin lambar yabon da yafi dadewa a duniya kuma aka fi girmamawa. An fara bayar da kyautan ne tun shekarar 1895.

Bangarorin rayuwa da bada lambar yabo kai sune ilmin likitanci, tattalin arziki, kwarewa a yare, kimiyya da fasaha.

Ana bada wannan lambar yabo ne ga kwararrun a wadannan bangarori da suka ciri tuta wajen kirkiro sabon abun inganta rayuwar al'ummar duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel