Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram 15 a Borno

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram 15 a Borno

Dakarun sojojin Najeriya na 242 Bataliya tare da sojojin Sector 2, MNJTF da dakarun sojojin kasar Chadi, CDF sun afkawa 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe guda 15 daga cikin su a Borno.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa shugaban sashin yada labarai na rundunar sojojin, Kwanel Aminu Iliyasu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a a Abuja.

Mista Iliyasu ya ce sojojin sun afka wa 'yan ta'addan ne a kauyen Jigalta a ranar Alhamis kusa das Marari kilomita 27 daga Monguno a Borno yayin da suke sharan fage.

Ya ce 'yan ta'addan sunyi kwanton bauna ne da motocci masu dauke da bindiga 5 amma ba a tabbatar da adadinsu ba.

DUBA WANNAN: Tausayi: Bidiyon yadda Sarki Sanusi ya zubar da hawaye yayin bayar da labarin wata mata a Kano

A cewarsa, an kashe 15 daga cikin 'yan ta'addan yayin da wasu daga cikinsu suka tsere da raunin bindiga.

Ya ce, "Bugu da kari, an lalata motoccin su masu bindiga biyu an kuma kama biyu daga cikinsu.

"Kuma sojojin sun kwato bindigu masu harbo jiragen sama hudu, AK 47 guda 9 da kuma wasu alburusai.

"Sojan Najeriya guda daya ya rasu yayin musayar wutan yayin da sojan Chadi daya ya samu rauni."

Mista Iliyasu ya ce kwamandan Sector 3 na Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Abdulmalik Biu tare da wasu kwamandoji sun ziyarci sojojin a inda abin ya faru.

A cewarsa, Mista Biu ya yaba da kokarin sojojin kuma ya isar da sakon shugaban hafsin sojojin kasan Najeriya, Lt-Janar Tukur Buratai da kwamandan MNJTF, Manjo Janar Chikezie Ude na yabo da jinjina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel