Yanzu Yanzu: Dino Melaye ya yi martani bayan ya tabbata kotu ta kwace kujerarsa na Sanata

Yanzu Yanzu: Dino Melaye ya yi martani bayan ya tabbata kotu ta kwace kujerarsa na Sanata

Sanata Dino Melaye mai wakiltan yankin Kogi ta yamma ya tabbatar da shan kaye da yayi a kotun daukaka kara bayan kotun zaben sanata na jahar ta soke nasarar zabensa.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na twitter Dino ya bayyana cewa a kowani hali, shi ya kasance mai mika godiya ga Allah.

Ya kara da cewa shakka babu duk wanda ya fara aikin alkhairi toh dole sai ya kammala shi. Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su kasance masu bin doka domin za su cimma nasara.

Ga yadda ya wallafa a shafin nasa: “Yanzun nan na rasa zabena a kotun daukaka kara sannan anyi umurnin sake sabon zabe. A dukkan yanayi ina mai mika godiya ga Allah. Duk wanda ya fara aikin alkhairi shakka babu zai kammala shi. Ina kira ga magoya bayana da su kasance masu bin doka domin za mu shawo kan lamarin a koda yaushe. Godiya ya tabbata ga Allah."

Legit.ng ta rahoto cewa Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kotun zabe wacce ta fitittiki Sanata Dino Melaye matsayin sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma.

KU KARANTA KUMA: Babu auren da shugaba Buhari zai yi a yau – Femi Adesina

Kotun ta bada umurnin gudanar da sabon zabe a yankin.

Bayan hukuncin kotun farko, Dino yace wadanda suka shigar da kararsa sun yi karairayi da dama a gaban kotun, tare da hada karya da gaskiya duka suka fada ma kotun, don haka yake a yanzu haka lauyoyinsa sun fara nazarin hukuncin don shirya yadda zasu daukaka kara game da lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel