Babu auren da shugaba Buhari zai yi a yau – Femi Adesina

Babu auren da shugaba Buhari zai yi a yau – Femi Adesina

A ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoba ne wani labari ya dunga yawo a kafafen sadarwa cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai auri ministar kula da harkokin agaji da annoba, Misis Sadiya Umar Farouq, a matsayin mata ta biyu.

Harma aka yi ikirarin cewa wata majiya kusa da fadar Shugaban kasa tace za a daura auren ne a ranar yau Juma’a, 11 ga watan Oktoba.

Sai dai kuma jaridar Tribune ta ruwaito cewa ta kira hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman a kafofin watsa labarai, Mista Femi Adesina domin tabbatar da gaskiyar lamarin, inda shi kuma ya yi watsi da labarin. Adesina yace kawai yaudara ce daga wadanda suka kagi labarin na karya.

Ya bayyana cewa labarin ba komai bane face karya sannan kuma cewa babu wani batun aure makamancin haka da zai gudana a fadar Shugaban kasa a ranar Juma’a.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari tayi kira ga daukar matakin gaggawa domin kare mutuncin yara mata

Har ila yau, wata majiya daga fadar Shugaban kasa a safiyar ranar Juma’a tace babu wani aure da zai gudana a fadar Villa, ko kuma shirin wani aue na Shugaban kasa Buhari a Aso Rock.

Yace labari da ke yawo a shafukan sadarwa duk kanzon kurege ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel