Yanzu-yanzu: Shikenan, kotu ta kwace kujerar Sanata Dino Melaye

Yanzu-yanzu: Shikenan, kotu ta kwace kujerar Sanata Dino Melaye

]Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kotun zabe wacce ta fitittiki Sanata Dino Melaye matsayin sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma.

Kotun ta bada umurnin gudanar da sabon zabe a yankin.

Bayan hukuncin kotun farko, Dino yace wadanda suka shigar da kararsa sun yi karairayi da dama a gaban kotun, tare da hada karya da gaskiya duka suka fada ma kotun, don haka yake a yanzu haka lauyoyinsa sun fara nazarin hukuncin don shirya yadda zasu daukaka kara game da lamarin.

“Ina da tabbacin kotun daukaka kara za ta canza wannan hukunci, amma duk da haka ina jinjina ma babban Alkalin kotun daya yanke hukuncin saboda tsaya ma gaskiya da ya yi, kuma ina kira ga duk masu farin cikin an kayar dani zabe su sani murnarsu za ta koma ciki.” Inji shi.

Daga karshe Sanatan ya yi kira ga masoyansa dasu zauna cikin kwanciyar hankali ba tare da tayar da hankali ko rikici ba, sa’annan ya basu tabbacin babu wanda ya isa kwace amanar da suka bashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel