Aisha Buhari tayi kira ga daukar matakin gaggawa domin kare mutuncin yara mata

Aisha Buhari tayi kira ga daukar matakin gaggawa domin kare mutuncin yara mata

Uwargidar Shugaban kasa, Aisha Buhari, tayi kira ga ayi gaggawan daukar matakin kare yara mata daga cin zarafi.

Aisha a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na twitter a ranar Juma’a, 11 ga watan Oktoba domin tunawa da ranar yara mata na duniya a Abuja, ta bayyana bukatar ganin iyaye sun kare yaransu daga duk wani rikici da cin zarafi.

Taken bikin ranar yara mata na 2019 shine: Girl Force: ” Unscripted and Unstoppable”.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN)ta ruwaito cewa an fara raya wannan rana da majalisar dinkin duniya ta kaddamar a matsayin ranar yara mata ne a ranar 11 ga watan Oktoba, 2012.

Wannan ya sake ba yara mata dama sosai da kuma Karin wayar da kai akan rashin daidaiton jinsi da mata ke fuskanta a fadin duniya saboda jinsinsu.

Aisha Buhari ta nuna jindadi akan cigaban da kungiyoyin mata ke samu kan bukatar kare kansu daga duk wani rikici da ya shafi jinsi.

KU KARANTA KUMA: Daukar aiki: Hukumar sojin ruwa ta saki sunayen wadanda suka yi nasara, ta yi karin bayani

“Ina farin cikin lura da cigaban da aka samu a bangaren fafutukar mata domin kare jinsin su.

“Ina son bayyana cewa akwai bukatar kara kaimi sosai musamman ta bangaren magance ikicin jinsi sannan ya zama dole a hada hannu domin cimma wannan.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel