Yayinda ake yada jita-jitan daurin aurenta da Buhari, Sadiya na Amurka

Yayinda ake yada jita-jitan daurin aurenta da Buhari, Sadiya na Amurka

Yayinda yan Najeriya ke cigaba da yada jita-jitan karya cewa shugaba Buhari zai yi sabuwar amarya yau, Ministar bada tallafi da manajin annoba, Sadiya Umar Farouq, tana birnin New York, kasar Amurka domin halartan taron majalisar dinkin duniya.

A wani jawabi shafin Tuwita, ministar wacce ake rade-radin cewa itace sabuwar amaryar daurin auren da za'a gudanar a ya Juma'a, ta saki jawabin kira ga yan Najeriya kan yadda za'a kawar da talauci.

Tace: "A ranar 17 ga Oktoba, ku hada kai da mu wajen kawar da taluci. Ranar kawar da Talauci da ake murnar zagayowarsa na kwadaitar da mutane ne wajen mutunta mutanen da ke rayuwa cikin bakin talauci."

Amma duk da haka, yan Najeriya a shafin Tuwita da sauran kafafen ra'ayi da sada zumunta basu daina maganar daurin aurenta da Buhari ba.

Martani kan jawabin da tayi, wasu yan Najeriya sun yi kira da ita tayi sauri ta dawo Najeriya yau saboda komai ya kankama domin daurin aurenta.

Kalli jawaban::

Asali: Legit.ng

Online view pixel