Kasar Birtaniya ta yi alkawarin taimakawa Najeriya wajen yakan Boko Haram

Kasar Birtaniya ta yi alkawarin taimakawa Najeriya wajen yakan Boko Haram

Gwamnatin kasar Birtaniya ta yi alkawarin taimakawa hukumar sojin Najeriya wajen yaki da yan ta'addan Boko Haram ta hanyar tallafa musu da makamai da kayayyakin yaki.

Sabon mai bada shawaran tsaron Birtaniya zuwa Najeriya, Mista Paul Warwick, ya bada wannan tabbaci ne yayinda ya jagoranci tawagar jakadun kasar Birtaniya zuwa hedkwatan hukumar Spjin Najeriya biyo bayan gayyatar babban hafsan sojin kasa, Laftanan janar Tukur Buratai, ranar Alhamis.

Paul Warwick ya bayyana cewa alakar Najeriya da Birtaniyya na da amfani saboda kasashen biyu na da tarihin alaka ta tattalin arziki.

KU KARANTA: Dukkan dukiyoyin da muka kwato sayar da su zamuyi - Buhari

Yace: "Mun zo nan ne domin kaddamar da tattaunawa da zai taimakawa hukumar Sojin Najeriya da sauran jami'an tsaro wajen samun nasara kan yan ta'adda da yan baranda. "

"Hazakalika mun zo tattaunawa ne da masu ruwa da tsaki a gwamnatin Najeriya kan habaka tattalin arzikin kasa."

Babban hafsan sojin kasa, Laftanan janar Tukur Buratai, ya ce taimakon makamai yaki da gwamnatin Birtaniya ke yi zai cigaba da zurfafa alakar kasashen biyu.

A wani labarin daban, dakarun soji Najeriya sun damke daya daga cikin yan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, Abdullahi Modu, wanda ya shahara da tuka motan baro jiragen sama.

An damke wannan kwamanda ne tare da wasu yan ta'addan guda tara a Pulka, jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel