EFCC ta kara kwace kadarorin makuden kudade na tsohon shugaban hukumar fansho

EFCC ta kara kwace kadarorin makuden kudade na tsohon shugaban hukumar fansho

- Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta mika bukatar kwace wasu kadarorin makuden kudade da ta gano na da dangantaka da Maina

- An gano kadarori masu dumbin yawa a kasashen ketare wadanda suke mallakin tsohon shugaban hukumar fanshon

- EFCC ta bankado wasu asusun bankuna da Maina ke amfani dasu amma an budesu ne ba da sunansa ba

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta mika bukatarta gaban kotu na kwace wasu kadarori 29 na kimanin naira biliyan daya na Abdulrasheed Maina.

Maina, tsohon shugaban hukumar fansho, an kamasa ne a otal a Abuja cikin watan Satumba yayin da ya shigo kasar cikin sirri daga Dubai inda ya koma zama.

An kamasa ne da dansa, Faisal, wanda ya fito da bindiga don hana kama mahaifinsa.

Tun bayan kama Maina, hukumar yaki da rashawa ta EFCC ke ta masa tambayoyi.

KU KARANTA: El-Rufai ya dauki mataki nan take bayan an sanar da shi cewa Jami'ar Kaduna ta dauki malamin da aka kora saboda lalata da mata aiki

Wasu kadarori a kasashen ketare da ake zargin na Maina ne, duk an gano su Dubai.

Majiya kusa da masu binciken suna gano cewa, daga cikin abubuwan da aka samu daga Maida da dansa sun hada da layikan waya 31. Hakazalika an kamasu da wayoyin tafi da gidanka har 19. Sauran abubuwan da aka kamasu da su sun hada da iPad da laptop guda biyu.

Majiyar ta kara da cewa, akwai bayanan hannayen jari da kadarorin Maina na kasashen ketare. Shaidun wadannan kuwa na dauke da sunan dan Maina ne ba sunansa ba.

An gano kamfanin hayar motocin alfarma da kuma masana’antar tsaftace kayayyaki na Maina da suke Dubai.

Majiyar ta kara da cewa, kamfanin man fetur da iskar gas na Ostrich duk mallakin wanda ake zargin ne. Akwai kuma asusun banki da yawa da Maina ke amfani dasu amma ba da sunansa ba da hukumar EFCC din ta bankado.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel