Mun sauya tunanin tsaffin yan Boko Haram 281 - Hedkwatan hukumar Soji

Mun sauya tunanin tsaffin yan Boko Haram 281 - Hedkwatan hukumar Soji

Akalla tsaffin yan Boko Haram 281 aka horar na tsawon makonni 52 na sauya tunani da fikra karkashin shirin da hedkwatan hukumar soji dake Abuja ta shiryawa yan Boko Haram din da aka kama.

An gudanar da wannan shiri na tsawon shekara daya ne a jihar Gombe.

Hedkwatan hukumar ta bayyana hakan ne inda tace a fara wannan shiri ne daga shekarar 2015 domin kwadaitar da yan Boko Haramun dake shirin tuba.

Hukumar sojin ta kara da cewa an fara shirye-shirye daukan wasu sabbin yan Boko Haram da suka mika wuya 650 domin sauya tunani a fikransu.

KU KARANTA: Dukkan dukiyoyin da muka kwato sayar da su zamuyi - Buhari

Hedkwatar tace: "Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samar da shirin Operation Safe Corridor a Satumban 2015 domin kwadaitar da wadanda ke son tuba su mika wuya kuma su shiga shirin sauya tunaninsu, gyara rayuwarsu da kuma mayar da shu cikin al'umma."

"Manufar wannan shirin shine rage yawan yan Boko Haram."

"Tsaffin mayakan zasu shiga shirin makonni 52 wanda ya kunshi wa'azuzzuka, sauya tunani, wasa, hadarin ta'amuni da kwayoyi, ilmin Boko da aikin hannu."

A yayin shirin, ana baiwa yan uwansu daman kawo musu ziyara kuma ana gayyato manya mutane.

A wani labarin daban, dakarun soji Najeriya sun damke daya daga cikin yan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, Abdullahi Modu, wanda ya shahara da tuka motan baro jiragen sama.

An damke wannan kwamanda ne tare da wasu yan ta'addan guda tara a Pulka, jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel