An yiwa wani dalibin jami'a korar kare saboda ya nuna adawarsa ga gwamnan Taraba a Facebook

An yiwa wani dalibin jami'a korar kare saboda ya nuna adawarsa ga gwamnan Taraba a Facebook

- An kori wani dalibin jami'ar jihar Taraba saboda ya bayyana ra'ayinsa da ya sha ban-ban dana gwamnan jihar a Facebook

- Dalibin dai ya bayyana wasu dalilansa da ya sa ya nemi gwamnan jihar ya tsaya da kokarin da yake yi na gina sabon filin jirgin sama a jihar

- Wannan ra'ayi da dalibin ya bayyana shine ya sanya kwamitin makarantar ta kore shi baki daya daga makarantar

Wani sabon dalibi da yake jami'ar jihar Taraba ya ga ta kanshi, bayan an kore shi daga jami'ar baki daya saboda ya ci mutuncin gwamnan jihar Darius Ishaku a shafin Facebook.

Dalibin da aka bayyana sunan shi da Joseph Israel, ya wallafa wata magana ta cin mutunci akan shirye-shiryen da gwamnan jihar yake yi na gyare-gyare da kuma gina sabon filin jirgin sama a jihar.

Dalibin wanda ya bayyana dalilansa da zai saka gwamnan tsayawa da wannan aiki na filin jirgin sama da ya saka a gaba.

A yadda rahoto ya bayyana an gurfanar da dalibin a gaban hukumar makarantar inda ake tuhumar sa da rashin da'a.

KU KARANTA: Bidiyo: Yayana ne ya fara sani na 'ya mace, gashi yanzu har yayi mini ciki, ina mafita - Inji wata budurwa

Dalibin ya ce a lokacin da hukumar makarantar ta fara tuhumar sa ya tambayesu shin akwai wata doka a makarantar da ta ce kada dalibi yayi amfani da shafukan sada zumunta wajen bayyana ra'ayinsu akan abubuwan da gwamnati take yi?

Ya kara da cewa kwamitin makarantar ba ta bashi amsar wannan tambayar da yayi mata ba. Ya ce kawai dai sunce mishi ya tafi har sai sun kammala gabatar da bincike akan wannan lamari, inda daga baya kuma suka ce sun kore shi baki daya ma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel