Tsaffin yan Boko Haram 2 sun fara karatun digiri a jami'a

Tsaffin yan Boko Haram 2 sun fara karatun digiri a jami'a

Shugaban kwamitin gudanarwan jami'ar National Open University of Nigeria, Farfesa Peter Okebukola, ya ce tubabbun yan Boko Haram biyu sun fara karatun digirinsu a jami'ar.

Ya bayyana hakan ne bayan ganawar kwamitin jami'ar a Abuja, ya kara da cewa mata sun fi maza shiga jami'ar.

A cewarsa, ya ce jami'ar ce makarantar da tafi yawan dalibai a Najeriya inda ta samu dalibai 550,000 kuma mata sun fi yawa.

Ya ce kwamitin ta bada damar fara sabbin tsangaya na karatun yaren Faransa, Majisteer da doktora a ilimin jarida, da sauransu.

A wani labari mai kama da haka, akalla tsaffin yan Boko Haram 281 aka horar na tsawon makonni 52 na sauya tunani da fikra karkashin shirin da hedkwatan hukumar soji dake Abuja ta shiryawa yan Boko Haram din da aka kama.

An gudanar da wannan shiri na tsawon shekara daya ne a jihar Gombe.

KU KARANTA: Mun sauya tunanin tsaffin yan Boko Haram 281 - Hedkwatan hukumar Soji

Hedkwatan hukumar ta bayyana hakan ne inda tace a fara wannan shiri ne daga shekarar 2015 domin kwadaitar da yan Boko Haramun dake shirin tuba.

Hukumar sojin ta kara da cewa an fara shirye-shirye daukan wasu sabbin yan Boko Haram da suka mika wuya 650 domin sauya tunani a fikransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel