Makonni 5 kafin zaben gwamna: Gwamnan PDP ya nada sabbin hadimai guda 60

Makonni 5 kafin zaben gwamna: Gwamnan PDP ya nada sabbin hadimai guda 60

Gwamna Seriake Dickson na jihar Bayelsa, ya sake nada masu bashi shawara na musamman su guda 60. Fidelis Soriewei, babban sakataren labaran gwamnan ne ya bayyana cigaban a wani jawabi dauke a sa hannunsa a ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoba.

Soriwei ya bayyana cewa sabbin hadiman da aka nada, wadanda aka debo daga kananan hukumomi takwas na jihar za su taimaka wa gwamnati wajen kammala mulki da kyau.

“Mai girma Gwamnan jihar Bayela, Henry Seriake Dickson, ya amince da nada sabbin masu bashi shawara na musamman su 60 duk a cikin kokarin ganin gwamnatin ta kammala mulki da kyau a jajircewarta na ganin ta isar da shugabanci yadda ya kamata ga mutanen jihar Bayelsa,” inji jawabin.

Nadin na zuwa ne yan makonni kafin zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Soriwei ya cigaba da cewa “gwamna ya umurci masu ruwa da tsaki da su zabi mata da za a baiwa mukami a matsayin hadimai na musamman a mako mai zuwa, a bangarorin da ba a basu mukamai ba."

KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya dauki mataki nan take bayan an sanar da shi cewa Jami'ar Kaduna ta dauki malamin da aka kora saboda lalata da mata aiki

Dickson, wanda zai kammala mulkinsa na biyu, na da sama da masu mukami 2000 a majalisarsa tun bayan da ya zarce a 2016.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel