Majalisar jihar Zamfara ta haramtawa 'yan majalisa tattauna matsalar tsaro a zauren majalisa

Majalisar jihar Zamfara ta haramtawa 'yan majalisa tattauna matsalar tsaro a zauren majalisa

- Majalisar jihar Zamfara ta hana tattauna matsalolin tsaron da ke addabar jihar a zauren majalisar

- Kakakin majalisar, Alhaji Nasiru Magarya ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar da aka yi a jiya Alhamis

- Shugaban masu rinjye na majalisara, ya ce, za a danganta hikimar yin hakan ne da rashin son fallasar matakin da gwamnatin jihar ke dauka akan tsaro

Kakakin majalisar jihar Zamfara, Alhaji Nasiru Magarya a ranar alhamis ya jaddada cewa, majalisara jihar bazata cigaba da tattauna matsalolin tsaro a zauren majalisar ba.

Magarya ya sanar da hakan ne ga ‘yan majalisar a ranar Alhamis yayin zaman tattaunawa da ‘yan majalisar.

KU KARANTA: Abubuwan da yakamata ku sani game da 'yar jaridar da ta bankado asirin malaman jami'a

Yace, akwai abubuwan da bai kamat ana bayyana sub a sai a taron sirri da kwamitin tsaro na majlisar.

Kakakin na maida martini akan zancen da dan majalisar jihar mai wakiltar Bukkuyum ta kudu, Alhaji Dahiru Adafka ya tada akan kalubalen tsaro da ke addabar mazabarsa.

Tuni dama shugaban masu rinjaye na majalisar,Alhaji Faruk Dosara, yayin tunatar da majalisar, y ace dama can anyi yarjejeniyar cewa an daina tattauna matsalar tsaro a zauren majalisar gani da cewa matsala ce da ke bukatar sirri.

”A tunani na, tuni dama mun amince da cewa, mun dena tattauna matsalar tsaro a yayin zaman majalisar ganin cewa matsala ce da ke bukatar sirri. Mun dau wannan matakin ne don hana fallasar abinda gwamnatin jihar ta yanke ga jama’a”. In ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel