Majalisar jihar Legas ta yi barazanar kama tsohon gwamnan jihar

Majalisar jihar Legas ta yi barazanar kama tsohon gwamnan jihar

- Kakakin majalisar jihar legas ya baiwa magatakardar majalisar umarnin rubuta wasikar gayyata ga tsohon gwamnan jihar don zuwa tattaunawa da majalisar akan sayen ababen hawa 820

- Ya kara da bada umarnin gayyato duk jami'an gwamnati da ke da hannu a cikin lamarin

- Majalisar ta yanke hukuncin cewa, matukar suka ki amsa gayyatar zata wallafa a jaridu inda daga baya zatta bada damar a cafkosu

Kakakin majalisar jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya bukaci magatakardan majalisar, Azeez Sanni, da ya gayyaci tsohon gwamnan jihar, Akinwunmi Ambode akan ababen hawa 820 da aka siya yayin mulkinsa.

Obasa ya kara da bada umarnin gayyato duk tsoffin jami’an gwamnatin da ke da sa hannu a wannan aikin a wancan lokaci.

Yace, idan suka ki amsa gayyatar, majalisar zata wallafa a jaridu inda daga baya zata nemi yardar kamasu.

Kakakin majalisar ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin tataunawa da kwamiti biyu na wucin gadi na majalisar.

KU KARANTA: Abubuwan da yakamata ku sani game da 'yar jaridar da ta bankado asirin malaman jami'a

Shugaban kwamitin mutum 9 da majalisar ta nada don binciko yadda siyan ababen hawan ta kama. Fatai Mojeed, y ace a cikin jami’ai 20 da majalisar ta gayyata, 4 daga ciki basu amsa gayyatar ba.

Ya bayyana cewa, daga cikinsu akwai: Tsohon kwamishina shari’a, Kazeem Adeniji, tsohon kwamishinan kasafin kudi, olusegun banjo, tsohon kwamishina kudi, Akinyemi Ashade da tsohon kwamishina wutar lantarki da ma’adanai, Wale Oluwo.

Daga rahoton da suka samu, wasu daga cikin ‘yan majalisar sun bada shawarar cewa a nemi yardarm kotu don kama tsohon gwamnan da kwamishinonin da abun ya shafa.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar ma sunce kundin tsarin mulki ya yarjewa majalisar da ta bada wannan damar. Amma daga baya majalisar ta yanke hukuncin cewa a kara basu dama ta hanyar rubuta wasikar gayyata garesu. Idan kuma basu amsa gayyatar ba, a wallafa a jaridu inda daga baya sai a kamasu idan basu hallara ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel