Za a fara cin tarar N5m ga kafafen yada labarai masu yada kalaman batanci, in ji Lai Mohammed

Za a fara cin tarar N5m ga kafafen yada labarai masu yada kalaman batanci, in ji Lai Mohammed

- Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce akwai kafafen yada labarai masu yayata kiyayya za a fara cinsu tarar miliyan biyar

- Ministan ya ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aminta da a kara duba tsohuwar dokar da ta aminta da cin tarar dubu dari biyar

- Hakan kuwa zai kawo karshen yada labaran kiyayya ko tsokacin wulakanci a kafafen yada labarai

Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aminta da a kara duba dokokin da kuma tarar da ake cin masu yada kalaman batanci ko tsokacin wulakanci a kafafen yada labarai.

Ministan ya sanar da hakan ne a Abuja yayin rantsar da kwamitin tabbatar da gyare-gyaren da aka yi na NBC.

KU KARANTA: Hukumar ‘yan sanda zata tura jami’ai 25,000 don bada tsaro a zaben jihar Kogi

Ya ce, abinda aka aminta dashi ya hada da cin gashin kan hukumar yada labaran ba tare da katsalandan din siyasa ba.

Ya ce, kwamitin zata kirkiro sabbin horo da tara da zasu yi daidai da na kasashen duniya, tabbatar da kwarewa da kuma ladaftar da masu karya doka.

Kwamitin ya samu shugabancin Farfesa Armstrong Idachaba.

A da hukuncin masu yada kalaman kiyayya da na batanci shi ne tarar naira dubu dari biyar. Amma a yanzu akwai yuwuwar a maida tarar naira miliyan biyar don ganin an kawo karshen ire-iren matsalolin nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel