Gwamnatin Buhari ko gandun barayi, inji jam’iyyar PDP

Gwamnatin Buhari ko gandun barayi, inji jam’iyyar PDP

Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce sake kama wani dan damfara wanda ke cikin gwamnatin Buhari ya sake tabbatar da cewa fadar shugaban kasan a karkashin jagoranci Shugaba Buhari, ba komi ba ce in banda dandazon barayi.

PDP ta ce kasancewar Iliyasu na da ofis tsundum a karkashin tsaron fadar shugaban kasa ta Villa abu ne wanda hankali ma ba zai iya dauka ba.

KU KARANTA:Neymar ya kafa wani babban tarihi a wasan kwallon kafan Brazil

A cikin wani zancen da mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar ranar Alhamis 10 ga watan Oktoba ya ce, Iliyasu ya jima yana tafka aika-aika daga bisa kujerar iko ta fadar shugaban kasa.

Wannan dalilin ne ya kara tabbatar da gwamnatin Buhari a matsayin wadda take cike da barayi masu dibar dukiyar jama’a a koda yaushe, a cewar Kola.

Har ila yau, jam’iyyar ta PDP ta kara da cewa babu abinda zai gagari gwamnatin dake cike da masu takardun karatu na bogi, masu laifukan cin-hanci da rashawa da kuma ministocin da ake tuhuma da rashawa da dama.

Ga abinda jam’iyyar ta fadi cikin zancenta: “Muna cike da mamakin ganin jam’iyyar dake ikirarin rikon amana da gaskiya, sai ga shi anata kama ‘ya’yanta da laifukan cin-hanci da rashin gaskiya iri daban-daban.

“Ko mako guda ba ayi ba, da aka damke wani na kusa da shugaban kasa mai suna, Nasir Danu a filin jirgin Hearthrow dake kasar Ingila, inda ake zarginsa da daukar fasfon kasa da kasa na bogi da kuma satar wasu makudan kudade.”

“Sai kuma ga shi an sake samun wani, Abdulrauf Iliyasu da laifin mai kama da na Nasir Danu. Ko shakka babu bamu taba samun gwamnatin da tayi fice wurin cin-hanci ba irin wannan a Najeriya.” Inji PDP.

https://thenationonlineng.net/buhari-presidency-a-den-of-thieves-says-pdp/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel