Jigo a APC ya tona asirin gwamnan jam'iyyar da ke kulle-kullen canja sheka

Jigo a APC ya tona asirin gwamnan jam'iyyar da ke kulle-kullen canja sheka

Dan takarar gwamnan jihar Edo a jam'iyyar APC, Manjo Janar Charles Airhiavbere (mai ritaya) ya zargi gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da kulle-kullen canja sheka zuwa wata jam'iyyar.

Janar Airhiavbere ya ce Obaseki na son canja sheka wata jam'iyyar da zai sake yin takara a karo na biyu bayan ya fuskanci cewa zai yi wuya ya sake samun tikitin takara a APC.

Da yake magana da manema labarai a birnin Benin, Airhiavbere ya ce jam'iyyar APC ta fara samu rigingimu a jihar Edo ne bayan zaben shugaban kasa.

Airhriavbere ya bayyana cewa rashin tabuka wani abun arziki a gwamnati ne silar batawar Obaseki da Adams Oshiomhole, shugaban jam'iyyar APC na kasa.

"Tun bayan zaben shugaban kasa babu wata gwamnati a jihar Edo, jam'iyyar adawa za ta karbar mulki cikin ruwan sanyi a hannunsa idan muka zuba ido.

DUBA WANNAN: Tikar rawa da mace: Sheikh Daurawa ya magantu a kan bullar wani faifan bidiyo da ake zaton shine ke cashe wa

"Zance ya gama kewaya gari cewar yana kulle-kullen canja sheka domin ya samu damar yin takara, hakan ne yasa ba ya son kan shugabannin jam'iyyar APC a jihar Edo ya hadu, bai damu da hadin kansu ba," a cewar Airhriavbere.

An dade da fahimtar cewa akwai baraka a tsakanin Oshiomhole da gwamna Obaseki, lamarin da wasu ke ganin zai yi wuya gwamnan ya sake samun tikitin takara a karkashin inuwar jam'iyyar APC da Oshimhole ke shugabanta a kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel