'Yan ta'adda sun kai hari a Borno yayin da 'yan majalisa suka ziyarci jihar

'Yan ta'adda sun kai hari a Borno yayin da 'yan majalisa suka ziyarci jihar

Wasu da ake zargin 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a karamar hukumar Gubio na jihar Borno.

Harin na zuwa ne a ranar Alhamis yayin da wata kwamitin hadin gwiwa na majalisar tarayya kan rundunar sojoji suka ziyarci jihar.

'Yan ta'addan sun iso garin da yamma suna da harbe-harbe wadda hakan ya jefa mazauna garin cikin dimuwa da fargaba.

Majiya daga hedkwatan sojoji ta shaidawa Channels Television cewa an aike da tawagan sojoji zuwa garin cikin gaggawa domin su taka wa 'yan ta'addan birki.

A cewarsu, sashin kai hari da jiragen yaki na Operation Lafiya Dole ba su samu damar kai hari ba saboda rashin kyawun yanayi.

DUBA WANNAN: Tausayi: Bidiyon yadda Sarki Sanusi ya zubar da hawaye yayin bayar da labarin wata mata a Kano

Babban kwamandan 7 Division, Brig Janar Abdul-Khalifa Ibrahim shima ya tabbatar da harin.

Sai dai ya ce dakarun sojojin sun dakile harin bayan sun isa garin sun fattaki 'yan ta'addan.

Brig Janar Ibrahim ya ce har yanzu ba zai iya bayar da cikaken bayani ba a yanzu domin ba a kammala fatattakan 'yan ta'addan ba.

A 'yan kwanakin nan 'yan ta'addan sun kai hare-hare da dama a garin na Gubio mai nisan kilomita 84 daga Maiduguri, babban birnin jihar.

An kai harin ne ba baya-bayan nan yayin da Manjo Janar Olusegun Adeniyi, Brig Janar Ibrahim da wasu manyan shugaban soji suka karbi bakuncin tawagar 'yan majalisa.

'Yan majalisar sun kai ziyarar ne karkashin jagorancin Sanata Ali Ndume da Hon. Abdulrazak Namdas inda aka zaga da su wurare daban-daban da sojojin ke ayyukansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel