Dukkan dukiyoyin da muka kwato sayar da su zamuyi - Buhari

Dukkan dukiyoyin da muka kwato sayar da su zamuyi - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa dukkan dukiyoyin da aka kwato hannun ma'aikatan gwamnatin da suka gaza bayyana yadda suka tara ba za'a mayar musu da shi ba.

Buhari ya ce sayar da su za'ayi kuma a zuba kudin baitul mali.

Shugaba Buhari ya ce a baya, dukiyoyin da aka kwace wajen barayin gwamnati ana mayar musu dashi muddin aka smau canjin mulki. Ya lashi takobin cewa hakan ba zai sake faruwa ba.

Ya ce tuni ya bada umurnin sayar da su tare da zuba kudin baitul malin gwamnati na asusun bai daya TSA.

Yace: "Bari mu gan wanda zai kwashe kudin yanzu daga baitul mali ya mayarwa wadannan mutanen kamar yadda aka dade anayi a da."

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayinda ya karbi bakuncin kwamitin bashi shawara kan yaki da rashawa PACAC a fadar shugaban kasa Abuja.

KU KARANTA: Yan mata masu jima'i da namiji fiye da daya na iya kamuwa da cutan dajin mahaifa (kansa) - Likitan mata ya yo gargadi

Buhari ya yi alkawarin cewa zai yi iyakan kokarinsa wajen rage kudin da ake biyan ma'aikatan gwamnati kuma ya tuge tushen rashawa duk inda yake.

Shugaban kasan ya yabawa mambobin kwamitin kan namijin kokari da sadaukar da kan da sukayi wajen amincewa da bautawa kasarsu.

Shugaban kwamitin PACAC, farfesa Itse Sagay wanda ya jagoranci tawagar ya ce Najeriya bata taba sa'an shugaba irin shugaba Buhari ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel