Toh fah: Dattawan yankin da Dino ke wakilta sun marawa tazacen Gwamna Bello baya

Toh fah: Dattawan yankin da Dino ke wakilta sun marawa tazacen Gwamna Bello baya

Dattawan yankin Kogi ta yamma karkashin inuwar Kogi West Elders Forum (KWEF) sun jaddada goyon bayansu ga tazarcen Yahaya Bello a matsayin gwamnan jihar.

A cikin wata takarda da aka saki a karshen wani taro tare da gwamnan a ofishin jamiín hulda da jama’a na jihar a Abuja a ranar Lahadi, dattawan sunce sun yanke shawarar ne bisa ra’ayin mutanen mazabar.

Dattawan yankin wadanda suka sanya hannu a takadar sune David Jemibewon, Abdullahi Mamman, Idris Yusuf Tawari, Ajayi Joseph, J.O.S Oshanupin, Funso Ako, Oluwayomi David Atte da kuma Olusegun Oloruntoba.

Sauran sun hada da Tunde Arosanyin, James Awoniyi, Bayo Ojo, babban lauyan Najeriya (SAN), Benjamin Taiwo, Funmi Bodunde, Dan Kunle, Isiaq Ajibola da kuma Deinde Abolarin.

A yanzu haka Sanata Dino Melaye na jam’iyar Peoples Democratic Party (PDP) ne ke wakiltan mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawa.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane da sauransu su 45 a Kaduna

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa sake ba gwamna Alhaji Yahaya Bello da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) damar mulki a karo na biyu daidai yake da kawo karshen jihar Kogi.

Dan takarar gwamnan na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben fidda gwani da aka yi kwanan nan ya bayyana hakan ne a Kabba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel