WAEC ta nada sabon rijistara

WAEC ta nada sabon rijistara

Hukumar tsara jarrabawar kammala makarantar sakandire ta kasashen Afrika ta yamma (WAEC) ta amince da nada Mista Pateh Bah a matsayin sabon rijistara da zai yi wa'adin zango daya mai tsawon shekaru biyar.

Mista Bah, dan asalin kasar Gambia, ya fara zangonsa a watan Oktoba kuma ya kare a watan Satumba na shekarar 2024.

Ya karbi kujerar daga hannun Dakta Iyi Uwadiae, dan Najeriya.

Mista Pateh Bar ya kammala karatun digirinsa na farko a shekarar 1997 a jami'ar 'Pune' da ke garin Maharashtra a kasar Indiya.

Ya kara zurfafa karatu a bangarorin ilimi daban-daban a jami'o'i da ke kasar Indiya da Ingila. Ya yi aiki a ma'aikatar Ilimi, matasa, wasanni da al'ada a Banjul, kasar Gambia, daga shekarar 1990 zuwa 1991 kafin daga bisani ya fara aiki da hukumar WAEC a shekarar 1991.

An nada shi a matsayin mataimaki na musamman ga rijistaran hukumar WAEC a shekarar 2002, lamarin da yasa ya koma hedikwatar hukumar WAEC da ke Accra, Ghana.

Ya yi aiki tare da rijistarori guda biyu a matsayin babban mataimaki, matsayin da aka fara nada shi a shekarar 2010.

Kwamitin zartar wa na hukumar WAEC ya amince da nadin Mista Bah a cikin watan Maris, 2019 yayin taronsa na shekara da aka yi a garin Freetown, kasar Sierra Leone.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel