Dan majalisar da aka kama a bidiyo yana karbar rashawa ya nemi kotu tayi watsi da tuhumar da ake masa

Dan majalisar da aka kama a bidiyo yana karbar rashawa ya nemi kotu tayi watsi da tuhumar da ake masa

- Tsohon shugaban kwamitin binciken tallafin man fetur na wucin gadi na majalisar wakilai, Farouk Lawan ya bukaci kotu ta sahale masa kare kansa

- Ana zargin Lawan ne da karbar cin hancin dala dubu dari biyar cikin dala miliyan uku da ya bukata don cire sunan kamfani Otedola daga wadanda ake zargi

- Lauyansa ya ce, ba a iya tabbatar da sahihancin ya karba cin hancin ko a'a daga bidiyon da aka mika gaban kotun

Farouk Lawan, tsohon shugaban kwamitin wucin gadi akan binciken tallafin mai na majalisar wakilai, ya ce babu bukatar ya kare kansa a game zarginsa da ake da karbar hancin dallar amurka miliyan 3.

Lawan, ta hannun lauyansa, Mike Ozekhome, ya mika bukatar ne a gaban Mai shari'a Angela Otaluka a ranar Alhamis.

Ozekhome ya musanta cewa hukumara yaki da rashawa mai zaman kanta ta ICPC, ta kasa bayar da kwakwarar shaida a kan zargin da takewa wanda ke kare kansa.

DUBA WANNAN: Mataimakin gwamna ya kama direbobi da dama masu saba dokokin tuki (Hotuna)

Ya kara da cewa, masu karar sun bayar da bayanai mabanbanta akan yawan kudin da ake zargin Lawan da karba.

Ozekhome ya kara da cewa, bidiyon da masu karar suka gabatar disasshe ne a don haka ne ba a samu damar tantance gaskiyar lamarin ba.

Ya ce, kin kama Lawan da hukumar jami'an farin kaya (DSS) tayi kadai ya isa ya tabbatar da cewa babu gamsasshiyar shaida.

Lauyan masu kara, Adegboyega Awomolo, SAN, ya soki bukatar.

Ya sanar da kotun cewa, kin yarda da bidiyon da masu kara suka gabatarwa kotu da masu kare kansu suka yi bai isa ya zamo shaidar da za a ce bidiyon ba gaskiya bane kuma abinda ke ciki bai faru ba.

Ya kara da cewa, ya tabbatarwa da kotu cewa , Lawan ya karbi kudi don yin aikin da dama can ya rataya a wuyansa.

Mai shari'ar ya dage cigaba da sauraron karar zuwa 17 ga watan Oktoba inda zai yanke hukunci akan bukatar mai kare kansa.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa, an gurfanar da Lawan ne sakamakon zarginsa da ake da karbar dala dubu dari biyar cikin dala miliyan uku a matsayin cin hanci.

Ana zargin ya karbi kudin ne don zai cire sunan kamfanin Otedola daga jerin sunayen kamfanonin da majalisar ke tuhuma da badakalar kudin tallafin man fetur na 2012.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel