Gwamnatin tarayya da kamfanin CRCC na China za su shimfida layin dogo na $3.9bn daga Abuja zuwa Itakpe

Gwamnatin tarayya da kamfanin CRCC na China za su shimfida layin dogo na $3.9bn daga Abuja zuwa Itakpe

-Gwamnatin tarayya ta kulla yarjejeniyar shimfida layin dogo ta $3.9bn tun daga Abuja har zuwa Itakpe na jihar Kogi da wani kamfanin China

-Kamfanin CRCC shi ne zai cigaba da cin moriyar layin dogo har na tsawon shekara 30 kafin ya dawo mallakin Najeriya

Gwamnatin tarayyar Najeriya a ranar Alhamis 10 ga watan Oktoba, 2019 ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar $3.9bn da wani kamfanin kasar China mai suna China Railway Construction Corporation (CRCC) domin shimfida layin dogo daga Abuja zuwa Itakpe ta jihar Kogi.

Daga cikin aikin da za ayi har da ginin tashar jiragen ruwa a Warri ta jihar Delta. Wannan aikin na yarjejeniya ne tsakanin gwamnati da kamfanin mai zaman kansa, inda gwamnatin tarayya za ta biya kashi 15% yayin da kamfanin CRCC zai biya 10%.

KU KARANTA:Yara 102,000 ke mutuwa duk shekara sakamakon rashin tsaftar muhalli – Minista

Sauran kashi 75% din kuwa za a nemo su ne ta hanyar wani rance na musamman da gwamnatin tarayya ke yi a karkashin tsarin ciyo bashi na musamman wato Special Purpose Vehicle (SPV).

Bayan an kammala layin dogo kamfanin CRCC ne zai cigaba da gudanar da lamuran jiragen kasan da kuma layin na dogo har tsawon shekara 30. Idan aka kammala biyan bashin na kashi 75% sai ta mikawa gwamnatin Najeriya komi da komi.

Ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya yi bayani a kan abinda ya sanya gwamnati ta zabi yin amfani da yarjeniyar hadin gwiwa tsakanin kamfani mai zaman kansa da kuma ita gwamnatin.

A cewarsa, a zabi wannan tsarin yarjejeniyar ne saboda rage yawan ciyo bashi wanda ya riga ya ma gwamnatin yawa a halin yanzu, inji Ministan.

Ministan yayi wannan jawabin ne a Abuja lokacin da ake rattaba hannu a kan yarjejeniyar aikin, inda W. Wenzhong mataimakin shugaban kamfanin CRCC ya jagoranci tawagar kamfanin kasar Chinan.

https://www.independent.ng/fg-crcc-sign-3-9bn-abuja-itakpe-railway-agreement/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel