Yan mata masu jima'i da namiji fiye da daya na iya kamuwa da cutan dajin mahaifa (kansa) - Likitan mata ya yo gargadi

Yan mata masu jima'i da namiji fiye da daya na iya kamuwa da cutan dajin mahaifa (kansa) - Likitan mata ya yo gargadi

Wani likitan mata, Adetola Olatunji, ya gargadi yan mata da su kuji jima'i suna masu kananan shekaru da kuma mazaje daban-daban saboda hakan na iya janyo cutar dajin mahaifa.

Adtola ya ce cutan dajin mahaifan abu ne wanda ya zama ruwan dare tsakanin yan matan zamani kuma kwayar cutar Human Papilloma Virus (HPV) ne ke janyoshi.

Farfesan ilimin kiwon lafiyan matan wanda yayi wannan bayani jiya a jami'ar Olabisi Onabanjo University, Ago – Iwoye, ya ce kwayar cutar HPV ne babban musabbabin kashi 99 na cutar dajin.

Ya kara da cewa shan maganin rigakafin ciitar kafin fara jima'i ka iya kare faruwan cutan.

A cewarsa, yara maza da mata masu shekara 11 ko 12 da haihuwa su samu wannan rigakafin kafin fara jima'i sbaoda rashin haka zai sanyasu cikin hadarin kamuwa da cutan.

Adetola ya baiwa yan matan shawaran cewa sun garzaya asibiti domin sanin shin suna dauke da wannan cuta domin kawar da shi da wuri kafin ya gagari magani.

Yace kudin ganewa bai da tsada saboda a asibitin jami'ar, N500 ne kacal.

Ya muddin ba'a maganceshi da wuri ba, jinyarshi idan ya gagari magani abune mai wuya kuma ba'a fiye samun nasara ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel