Farfesa Sagay ya bayyana abinda ake yi da kudaden da aka kwato daga hannun barayin gwamnati

Farfesa Sagay ya bayyana abinda ake yi da kudaden da aka kwato daga hannun barayin gwamnati

- Shugaban kwamitin bada shawara ga shugaban kasa a kan rashawa, Farfesa Sagay, ya bayyana cewa kudaden da ake karbowa hannun masu babakere ana zuba su a baitul mali ne

- Farfesa Sagay ya ce kwamitin ya samu cigaba mai dumbin yawa a yayin yaki da rashawa a fadin kasar nan

- Shugaban na kwamitin ya kara da jan kunne ga masu tunanin fadawa harkar rashawa da su canza tunani

Shugaban kwamitin bada shawara ga shugaban kasa akan rashawa, Farfesa Itsey Sagay, ya bayyana cewa, kudaden da aka samu a wajen yaki da rashawa a kasar nan ana zubasu ne a baitul malin kasar inda ake amfani dasu wajen kyautata rayuwar talakawa.

Ya kara da bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta kwato biliyoyin nairori daga 'yan Najeriyar da suka wawuri kudin kasa a cikin shekaru hudu da rabi da suka gabata.

Sagay ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyi daga manema labaran gidan gwamnati a ranar Alhamis a Abuja.

DUBA WANNAN: Mataimakin gwamna ya kama direbobi da dama masu saba dokokin tuki (Hotuna)

Ya ce, kwamitin ya samu cigaba mai dumbin yawa a yayin yaki da rashawa a fadin kasar nan.

Kamar yadda ya ce, "Abin farinciki a lamarin shine, kudaden da ake karbowa ana zuba su ne a baitul malin kasar nan inda ake amfani dasu wajen kasafin kudin duk shekara,"

"Toh idan kuka ji ana zancen ciyar da yaran makaranta miliyan 12 da abinci mai inganci, horar da matasa wajen koyon sana'o'i tare da biyansu N30,000 duk wata tare da basu bashi ba tare da ruwa ba don karfafa musu kananan sana'o'i, to amfanin kudaden kenan."

"Mun kuma kara karfafa hukumomin yaki da rashawar ta hanyar horar da jami'ansu yadda zasu tunkari matsaloli tare da mikasu gaban shari'a."

Ya ce, masu shari'ar har na kotun koli sun amfana da horarwar.

Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta yi nasarar toshe baraka da rashawa har ta fannin man fetur a kasar nan.

"A bangaren rashawa, abun zai bada mamaki idan aka gano cewa babu mai magana akan tallafin man fetur. A da, ana yin asarar kusan naira biliyan 400 duk shekara akan tallafin man fetur na bogi duk shekara. Amma a yanzu babu."

Shugaban ya kara da jan kunnen masu tunanin fadawa harkar rashawa da su sake tunani saboda an shimfida hanyoyin ganosu da kuma hukuntasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel