'Yan bindiga sunyi awon gaba da mutum 20 a kusa da Zuma Rock

'Yan bindiga sunyi awon gaba da mutum 20 a kusa da Zuma Rock

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace mutane fiye da 20 a kusa da Zuma Rock na jihar Neja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun ce mutanen da aka sace wadda suka hada da ma'aikatan gwamnati da 'yan kasuwa suna hanyarsu ta komawa gidajensu ne misalin karfe 8 a ranar Talata lokacin da suka ci karo da 'yan bindigan sanye da kayan sojoji kusa da shingen sojoji a garin.

An sako mutane tara daga cikinsu bayan kimanin awa daya lokacin da 'yan bindigan suka shigar da su cikin daji mai nisan kilomita 5 daga titin Abuja zuwa Kaduna suka tantance su.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa wasu daga cikin maharan suna sanye da kayan sojoji rike da bindigu yayin da wasu kuma na sanye da kayan farar hula dauke da adduna da sauran makamai na gargajiya.

DUBA WANNAN: Mataimakin gwamna ya kama direbobi da dama masu saba dokokin tuki (Hotuna)

Daya daga cikin wadanda aka sako da ya yi magana da Daily Trust a ranar Alhamis ya ce a lokacin da suka dawo kan titin, sun tarar da 'yan sanda da sojoji suna gadin motarsu da kayayakinsu.

Ya ce sun isa gida misalin karfe 11 na daren ranar da abin ya faru.

Kwamandan 'yan sandan Suleja, ACP Isa Rambo ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya kara da cewa bai san cewa har yanzu akwai wasu da ba a sako su ba.

Wata mai shago a kasuwar Wuse da ke Abuja ta tabbatar wa majiyar Legit.ng cewa mutane uku cikin 'yan kasuwar har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutanen.

Majiyar ta ce tuni dai masu garkuwa da mutanen sun fara tattaunawa da iyalan wadanda suke garkuwa da su kan kudin fansa da za a biya kafin a sako musu 'yan uwansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel