Gwamnan Kogi: Dawowar Gwamna Bello a karo na biyu daidai yake da kawo karshen jahar – Dino Melaye

Gwamnan Kogi: Dawowar Gwamna Bello a karo na biyu daidai yake da kawo karshen jahar – Dino Melaye

Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa sake ba gwamna Alhaji Yahaya Bello da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) damar mulki a karo na biyu daidai yake da kawo karshen jihar Kogi.

Dan takarar gwamnan na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben fidda gwani da aka yi kwanan nan ya bayyana hakan ne a Kabba.

Domin nuna jajircewarsa,Sanata Melaye ya bayar da gudunmawar naira miliyan bakwai ga kananan hukumomi bakwai da ke mazabar, inda ya bukace su da su habbaka kamfen din jam’iyyar a yankin.

Ya kun fada ma dan takarar jam’iyyar a zabe mai zuwa, Injiniya Musa Wada cewa ya mayar da hankalinsa akan sauran yankunan, domin Kogi ta Kudu na da duk abubuwan da ake bukata domin samun nasarar jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Kuma dai: Masu garkuwa da mutane sun sace jami’in tsaro, matarsa da dansa a birnin tarayya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya samu goyon bayan wata jigo a siyasar jihar gabanin zabewn gwamna da za a gudanar a jihar a ranar 18 ga watan Nuwamba.

Hajiya Halima Alfa, jigo a jam'iyyar APC kuma shugaban mata ta shiga jerin wadanda suke goyon bayan takarar gwamnan a karo na biyu.

Hajiya Alfa dai fitacciyar 'yar siyasa ce mai jama'a musamman a kauyuka a mazabar Kogi ta Gabas na jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel