Abinda Jonathan ya yi bayan gana wa da Buhari a Villa

Abinda Jonathan ya yi bayan gana wa da Buhari a Villa

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya ki yin magana a kan abinda suka tattauna yayin ganawarsa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadar shugaban kasa, Villa, da ke birnin tarayya, Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa ba a bayyana wa manema labarai dalilin ganawar Buhari da Jonathan ba, wacce ta dauki tsawon mintuna 15.

Jonathan ya gaisa ne kawai da manema kabarai yayin da Ambasada Lawal Kazaure, hadimin Buhari, ya raka shi wurin da motarsa ke jira.

Wannan shine karo na farko da tsohon shugaba Jonathan ya ziyarci fadar shugaban kasa Buhari tun bayan sake cin zabensa a karo na biyu.

DUBA WANNA: Tikar rawa da mace: Sheikh Daurawa ya magantu a kan bullar wani faifan bidiyo da ake zaton shine ke cashe wa

Jonathan ya ziyarci fadar shugaban kasa a kalla sau biyu a zagaye na farko na mulkin shugaba Buhari.

Tun kafin hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da sakamakon zaben shekarar 2015, Jonathan ya kira Buhari ya taya shi murnar lashe zaben kujerar shugaban kasa, duk da shi Buharin ya kayar a wancan lokacin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel