Babbar Magana: Majalisar dokokin Legas na shirin bayar da umurnin kama tsohon gwamnan jihar

Babbar Magana: Majalisar dokokin Legas na shirin bayar da umurnin kama tsohon gwamnan jihar

Akwai yiwuwar za a kama tsohon gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode da wasu mutane hudu da su kayi aiki a gwamnatinsa inda barazanar da majalisar dokokin jihar tayi ya zama gaskiya.

Legit.ng ta gano cewa 'yan majalisar sun dauki wannan matakin ne bayan samun rahotanni biyu daga kwamitocin wucin gadi ba bincike da aka kafa domin bincike kan motoci 820 da tsohon gwamnan ya saya da kuma nazarin kasafin kudin 2019.

Wadanda lamarin zai iya shafa sun hada da Kazeem Adeniji (Attoney Janar kuma kwamishinan shari'a), Olusegun Banjo (Kwamishinan kasafin kudi), Akinyemi Ashade (Kwamishinan kudi) da Wale Oluwa (Kwamishinan makamashi da sinadarai).

DUBA WANNAN: Mataimakin gwamna ya kama direbobi da dama masu saba dokokin tuki (Hotuna)

Ciyaman din daya daga cikin kwamitin, Fatai Mojeed wadda ya gabatar da rahoton kwamitin ya ce binciken da akayi kan sayan motoccin 820 a lokacin mulkin Ambode ya nuna cewa ba a biya ka'ida ba.

A cewar Hon Mojeed, Ambode yayi amfani da kudin Paris Club don sayan motoccin ba tare da amincewar majalisar dokokin jihar ba.

"Bai sanar da majalisar jihar ba kafin ya fara sayan motoccin. An kashe fiye da naira biliyan 48 don sayan motoccin bas din kuma aka kashe naira biliyan 22 domin shigo da su da biyan kudin kwastam. 520 cikin motoccin har yanzu suna tashan jirgin ruwa," inji Mojeed.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel