Za a fara bawa malaman makarantun gwamnati kyautar 'Data' kowanne wata - Ministan Ilimi

Za a fara bawa malaman makarantun gwamnati kyautar 'Data' kowanne wata - Ministan Ilimi

Adamu Adamu, ministan ilimi, ya ce ma'aikatarsa na aiki tare da hukumar kula da harkokin sadarwa a Najeriya (NCC) domin fara bawa malaman makarantun gwamnati kyautar 'Data', a kalla '1 gigabyte', kowanne wata.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a wurin taron ranar malaman makaranta da aka yi yayin hutun karshen mako.

Adamu Adamu, wanda Chukuemeka Nwajiuba, karamin ministan ilimi, ya wakilta ya ce bawa malaman kyautar 'Data' zai basu damar amfani da yanar gizo domin neman karin bayanan da zasu taimaka musu wajen aikinsu na koyar da dalibai.

Kazalika ya bayyana cewa gwamnati na duba yiwuwar bullo da tsarin inshora na dundundun ga malaman makarantun gwamnati wanda ko bayan mutuwarsu iyalansu zasu cigaba da cin moriyar tsarin.

"Gwamnati za ta biya wa malaman makaranta maza miliyan N1 a matsayin inshora, malamai Mata za a biya musu miliyan N1.2. Za a biya wa malaman kimiyya miliyan N1.5 a matsayin kudin inshora," a cewar ministan.

Da yake gabatar da jawabi a wurin taron, Abubakar Malami, ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarraya, ya jaddada bukatar daukan mutane masu hazaka da zurfin tnani a matsayin malaman makaranta.

A daya daga cikin labaran Legit.ng na ranar Laraba, majalisar dattijai ta fara tattauna wa a kan bukatar yin dokar hukunta lakcarorin da ke tilasta dalibai yin lalata da su domin basu gurbin karatu ko kuma basu maki a jarrabawa.

Mamba a majalisar dattijai kuma mataimakin shugaban majalisar, Ovie Omo-Agege (dan jam'iyyar APC daga jihar Delta), shine wanda ya fara gabatar da kudirin a lokacin waccan majalisar, majalisa ta 8.

Kudirin, wanda aka fara gabatar da shi a watan Oktoba na shekarar 2016, ya nemi a daure duk wani lakcara da aka samu da laifin neman daliba da lalata na tsawon shekaru biyar a gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel