Kuma dai: Masu garkuwa da mutane sun sace jami’in tsaro, matarsa da dansa a birnin tarayya

Kuma dai: Masu garkuwa da mutane sun sace jami’in tsaro, matarsa da dansa a birnin tarayya

Yan bidiga sun yi garkuwa da jami’in tsaro na Civil Defence tare da matarsa da dansa, a kauyen Dafara dake yankin hukumar Kuje a babban birnin tarayya, Abuja.

Jaridar Punch ta ahoto cewa yan bindigan har ila yau sun kashe wani memba na kungiyar yan banga wanda ya shige su a lokacin da suka kai hari a daren ranar Laraba.

Lamarin na faruwa ne kusan sa’o’i 72 bayan wasu yan bindiga sanye da kayan sojoji sun yi garkuwa da mutane tara a kauyen Pegi, mai tazaran kilomita kadan daga Dafara.Jami’in Civil Defence ya kasance cikin wadanda aka sace, yayin da suka raunata jami’i daya.

Wata majiya da ta bayyana sunanta a matsayin Laide tace lamarin ya auku ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Laraba a lokacin da yan bindigan suka kai hari kauyen ta daji sannan suka yi garkuwa da Jami’in NSCDC, matarsa da yaransa.

KU KARANTA KUMA: Assha: Wasu yan uwa 2 sun fille kan wani yaro domin siyar dashi kan N200,000

Ba a samu Kakakin rundunar yan sanda reshen birnin tarayya, DSP Anjuguri Manzah ba don samun karin bayani dangane da lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel