Matasa sun yiwa wata budurwa dukan kawo wuka bayan an zarge ta da sacewa wasu maza 3 mazakuta a cikin mota

Matasa sun yiwa wata budurwa dukan kawo wuka bayan an zarge ta da sacewa wasu maza 3 mazakuta a cikin mota

Fusatattun matasa a ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoba, sun far ma wata matashiya bisa zargin sace wa wasu mutane uku mazakutansu a wata motar BRT a tashar Onipanu da ke jihar Lagas, inda ta sha da kyar.

Wakilin kamfanin dillancin labaran Najeriya wanda ya bibiyi lamarin, ya rahoto cewa matashiyar ta sha da kyar a hannun matasan da fasinjojin motar BRT din bayan sun far mata da duka akan zargin.

Wata idon shaida kuma fasinja a motar, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta fada ma NAN cewa wani mutumi ne ya nemi agaji cewa mazakutansa ya bace bayan matashiyar ta taba shi a motar.

Ta kara da cewa sai kuma wasu maza biyu da ke tsaye kusa da mutumin na farko suka nemi doki cewa suma hakan ya cika dasu domin sun gaza jin motsin mazakutansu.

Idon shaidan ta kara da cewa dole direban motan ya dauki dukkanin mutanen da ke cikin motar zuwa ofishin yan sanda dake Onipanu domin shigar da kara.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Boko Haram 10 da aka dade ana nema sun shiga hannu

An tattaro cewa wani jami’in dan sanda da ba a bayyana ba, ya tabbatar da faruwar lamarin sannan cewa yan sanda na kan lamarin.

NAN ta ruwaito cewa an dauki mazajen da abun ya shafa su uku zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba domin tabbatar da ikirarinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel