Taraba: Mun samu matsalolin satar mutane har guda 100 a cikin wata 9 – Gwamna Ishaku

Taraba: Mun samu matsalolin satar mutane har guda 100 a cikin wata 9 – Gwamna Ishaku

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku a ranar Alhamis 10 ga watan oktoba ya ce a tsakanin Janairu zuwa Satumba an samu matsalolin satar bil adama har guda 100 a jihar Taraba.

Ishaku ya fadi wannan maganar ne a wurin wani taron atisaye na Rundunar sojin Najeriya ta Division 3 dake Jos, mai taken ‘Operation Ayem-Akpatuma na II’.

KU KARANTA:Abin babba ne: Gwamnatin Ekiti za ta fara hukunta masu aikata fyade ta hanyar yi masu dandatsa

Gwamnan ya ce 30 daga cikin satar mutanen an yi su ne a cikin watan Satumba, yayin da kuma ya kara da cewa iyalan wadanda abin ya faru da su sun kashe tsakanin miliyan N200 zuwa N250 a matsayin kudin fansa.

Bugu da kari, gwamnatin jihar ta samar da babura guda 26 da kuma motocin Hilux guda biyu ga hukumomin tsaro domin taimakawa gwamnatin tarayya tabbatar da tsaro a jihar, a cewar gwamnan.

Ishaku ya cigaba da cewa, yana da yakinin lallai dakarun sojin Najeriya za su yi iya bakin kokarinsu na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk wuraren dake fama da rashin tsaro.

A na shi jawabin, Manjo-janar Nuhu Anbazo wanda shi ne babban kwamandan rundunar sojin Division 3, Jos ya ce an kirkiri wannan atisayen ne domin hada tawaga mai karfi saboda tunkarar abubuwan dake aukuwa a kasar nan.

Birgediya janar Briggs Daniel shi ne ya wakilci kwamandan, inda ya ce da zarar tawagar ta soma aiki za a shiga farautar bata gari da kuma masu tayar da hankalin jama’a.

Kwamandan ya yabawa Gwamna Ishaku bisa gudunmuwar da yake badawa a bangaren hukumomin tsaro a jiharsa. Kuma ya fadi cewa an bude wannan atisayen ne a jihohin Taraba, Binuwe, Nasarawa da Kogi.

https://www.dailytrust.com.ng/taraba-records-100-kidnappings-in-9-months-gov-ishaku.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel