Hukumar ‘yan sanda zata tura jami’ai 25,000 don bada tsaro a zaben jihar Kogi

Hukumar ‘yan sanda zata tura jami’ai 25,000 don bada tsaro a zaben jihar Kogi

- Hukumar 'yan sandan Najeiya ta ce zata tura jami'anta 25,000 zuwa jihar Kogi

-Sifeta janar din 'yan sandan ya sanar da hakan ne a taron da yayi da INEC da kuma masu ruwa da tsakin jihar

- Ya kara da jan kunnen 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki akan tayar da tarzoma yayin ko bayan zaben

Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, mohammed Adamu y ace akalla jami’an ‘yan sanda 25,000 za a tura jihar Kogi don tabbatar da tsaro yayin zaben gwamnan jihar da za a yi a 16 ga watan Nuwamba.

Adamu ya bayya hakan ne a garin Lokoja a ranar Alhamis yayin taron da suka yi da hukumar zabe mai zaman kanta da masu ruwa da tsaki na jihar Kogi.

KU KARANTA: Wani malamin jami'a yace bidiyon fallassar da BBC ta yi kirkirarre ne

Sifeta janar din da ya samu wakilcin Abdulmalik Ali, ya ce , ‘yan sandan a shirye suke don bada tsaro da yakamat yayin zaben.

Ya ce, ‘yan sandan zasu nuna matukar kwarewarsu wajen da tsaro a zaben me gabatowa.

Sifeta janar din ya hori ‘yan siyasa da magoya bayansu da su cigaba da yakin neman zabensu cikin kwanciyar hankali da lumana. Y ace, ‘yan sandan da sauran jami’an tsaro bazasu yi kasa a guiwa ba gurin sabawa duk wanda zai tada hankali lokacin ko bayan zaben.

Sifeta janar din y ace, bayanan sirri sun iso musu cewa akwai sojan gona da ke dinka kayan jami’an tsaro don amfani dasu yayin zaben. A don haka ne ya ja kunnen bata garin da su guji shiga fadawa hannun hukuma yayin aikata wannan mummunan aikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel