Abin babba ne: Gwamnatin Ekiti za ta fara hukunta masu aikata fyade ta hanyar yi masu dandatsa

Abin babba ne: Gwamnatin Ekiti za ta fara hukunta masu aikata fyade ta hanyar yi masu dandatsa

Kari a kan daurin rai da rai, gwamnatin jihar Ekiti a wani shirin hadin gwiwa da ofishin uwargidan gwamnan jihar na kokarin yin kwaskwarinma ga dokar hukunta masu aikata laifukan fyade.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito cewa uwargidan gwamnan jihar, Mrs Bisi Fayemi na neman majalisar dokokin jihar ta yi kwaskwarima ga dokar ta shekarar 2011, ta hanyar sanya dandatsa a matsayin hukunci ga masu fyade.

KU KARANTA:Babu sassauci: Duk alkalin da yake da laifin cin-hanci ku miko min sunansa, sakon Alkalin alkalai ga NJC

Haka kuma NAN ta sanar damu cewa, an soma gudanar da zama na musamman game da wannan dokar a majalisar dokokin jihar dake Ado-Ekiti ranar Alhamis 10 ga watan Oktoba, 2019.

A wurin wannan zaman, kwamishinan shari’a na jihar, Mr Wale Fapohunda ya ce a cikin kwaskwarimar da ake shirin yi akwai dandatsa, gwaji a kan tabin hankali da kuma haramtawa masu laifin amfana da duk wani abu na gwamnati.

Ita kuwa uwargidan gwamnan Ekiti, Mrs Bisi Fayemi a nata jawabin cewa ta yi, ta jima tana karbar korafe-korafe game da fyade tun cikin shekarar 2018.

Kamar yadda ta fadi, wadannan laifukan sun fi shafar mata ne kasancewar ana yawan ci masu zarafi da kuma yi masu fyade ba tare da sonsu ba.

“Yiwa wannan doka garambawul zai yi matukar amfani domin dakile yinkurin duk wani mai irin wannan zuciya ta ketawa musamman mata haddinsu. Kuma babu wani wanda zai aikata laifin nan ya tafi salun-alun ba tare da an hukunta shi ba, ko dan gida wanene kuwa.” Inji uwargidan gwamnan.

https://punchng.com/ekiti-goes-tough-on-rapists-pushes-for-castration-psychiatric-test/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel