Tikar rawa da mace: Sheikh Daurawa ya magantu a kan bullar wani faifan bidiyo da ake zaton shine ke cashe wa

Tikar rawa da mace: Sheikh Daurawa ya magantu a kan bullar wani faifan bidiyo da ake zaton shine ke cashe wa

A ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoba, aka samu bullar wani faifan bidiyo da wasu jama'a suka bayyana cewa mutumin da ke tikar rawa tare da wata mata a cikinsa, Sheikh Daurawa ne.

Kafafen yada labarai da ma'abota amfani da dandali sada zumunta sun yada bidiyon tare da bayyana cewa Sheikh Daurawa ne ke tikar rawa tare da matarsa.

Sheikh Daurawa fitaccen malamin addinin Islama ne a garin Kano da ma fadin Najeriya, a saboda haka yana da mabiya da masu dumbin yawa.

Daga cikinirin dumbin mabiyan Malamin ne wani ya aika masa da faifan bidiyon da ake yada wa domin ya warware wa jama'a, musamman mabiyansa, gaskiyar batun faifan bidiyon.

DUBA WANNAN: An samu miliyan N135 a hannun janar din rundunar soji da ake tuhuma da karkatar da kudaden sojoji

Ga kuma abinda Sheikh Daurawa ya fada kamar yadda BBC Hausa ta wallafa a sakon sautin muryar Daurawa da ta wallafa a shafinta na Tuwita, "Assalamu alaikum wa rahamatullahi ta'ala wa barakatuhu. Yau muna 10 ga watan 10, 2019 wanda yazo daidai da 11 ga watan Safar, watan biyu, shekara 1441 bayan hijira.

"Ina nan kasar Saudiyya a garin Makkah yanzu haka, wani mutum ya turo min wani hoto da wani mutum haka, kamar suna rawa a wurin biki, kuma wani mutum ya yi posting cewa Malam Aminu Daurawa ne yake rawa da matarsa, to tsakani da Allah wannan mutum ba ni bane, kuma ban san waye ba. Watakila jama'a sun ga kamanmaceniya ne da aka samu na kamanni tsakanina da wannan mutumi na cikin bidiyo, shi yasa suke tunanin ko nine.

"Ba ni bane, kuma ban san waye ba, ban san a ina aka yi wannan bidiyo ba. Ina fata Allah ya tabbatar mana da alkhairi," a cewar Sheikh Daurawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel