Yadda shugaban hukumar kula da hada-hadar Fetur ya yi kunnen uwar-shegu da umarnin Buhari

Yadda shugaban hukumar kula da hada-hadar Fetur ya yi kunnen uwar-shegu da umarnin Buhari

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa hukumar dake kula da hada-hadar cinikayyar fetur wato PEF ta daukin nauyin wasu lauyoyi guda hudu zuwa taron Lauyoyi na kasa da kasa a Seoul, babban birnin Koriya ta Kudu.

Hakan kuwa da hukumar tayi ya saba doka da karya umurni da gargadin gwamnatin tarayya na cewa ta dakile yawan tafiye-tafiye barkatai, musamman na tafiya irin wannan taro.

Sakamakon kalubale da ake kan fuskanta na kudaden shiga asusun gwamnatin tarayya, sai ta soke duk wasu karikitan tafiye-tafiye da ma’aikatan gwamnati ke yi na halartan taruka, tun a shekarar 2015.

An tattaro cewa gwamnatin tarayya ta kafa cewa sai wata tafiya ko fita mai dalili ko matukar muhimmanci ce kadai za a iya amincewa a fita waje a halarta. Ita ma din, an bada gargadin cewa sai an nemi izini daga Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.

Cikin 2016 ne gwamnatin Buhari ta sake jaddada wannan mataki da gargadin hana ma’aikata fita waje taro, wanda tun a daidai karshen mulkin Jonathan cikin 2015 ne aka fito da umarnin.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa hukumar PEF ta yi wancakali da wannan gargadi na gwamnatin Shugaba Buhari, inda ta tura lauyoyi hudu kasar Koriya ta Kudu, suka halarci taro, ba tare da neman yardar Ofishin Shugaban Ma’aiktan Tarayya ba.

Majiyar tamu ta Premium Times ta kara da cewa daga cikin lauyoyin hudu, guda uku daga Ma’aikatar Shari’a aka dauki nauyin su. Ta kuma rahoto cewa Shugaban Hukumar PEF, Ahmed Bobboi ne ya sa hannun amincewa PEF ta dauki nauyin halartar lauyoyin taron, wanda aka gudanar a ranakun 22 zuwa 27 ga Satumba, 2019.

KU KARANTA KUMA: Babban magana: EFCC ta kama dan damfara a fadar shugaban kasa

Biyu daga cikin lauyoyin ma’aikata ne a Ma’aikatar Shari’a, biyu kuma na Ma’aikatar Man Fetur da PEF ne.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa an kashe akalla naira miliyan 11 wajen daukar nauyin lauyoyin fita waje domin halartar taron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel