Babu sassauci: Duk alkalin da yake da laifin cin-hanci ku miko min sunansa, sakon Alkalin alkalai ga NJC

Babu sassauci: Duk alkalin da yake da laifin cin-hanci ku miko min sunansa, sakon Alkalin alkalai ga NJC

Alkalin alkalan Najeriya, Mai-shari’a Tanko Muhammad ya bayyana shirinsa na yakar cin-hanci da rashawa a tsakanin alkalan Najeriya. Alkalin ya ce sam baya goyon bayan ayyukan rashawa.

Tanko ya yi kira ga hukumar NJC da ta miko masa sunan duk alkalin da yake da wani laifi na cin-hanci domin a zartar masa da hukunci. A cewar alkalin alkalan shugabancinsa bai son cin-hanci ko kadan.

KU KARANTA:Buhari ya gana da kwamitin shawara game da cin-hanci da rashawa a Villa

Jastis Muhammad ya kara da cewa, Kotun koli a shirye ta ke domin gudanar da aldaci ga ‘yan Najeriya ta hanyar bin dokokin shari’ar kasar nan.

Alkalin alkalan yayi wannan maganar ne ranar Laraba 9 ga watan Oktoba, 2019 a yayin da karbi bakuncin kwamitin bai wa shugaban kasa shawara a kan cin-hanci wadda suka kai masa a ofishinsa na Abuja.

Kamar yadda mai magana da yawun alkalin, Dr Akande Festus ya fitar cikin zancensa, Tanko ya sanar da kwamitin cewa kotun koli a ko da yaushe na shirye da sauraron korafe-korafe da suka shafi laifukan cin-hanci.

Shi kuwa shugaban kwamitin ba shugaban kasa shawara a kan cin-hanci da rashawa, Farfesa Sagay (SAN) a nasa jawabin, ya ce sun zo ofishin alkalin ne domin taya shi murna bisa wannan mukamin da ya samu, inda ya ce hakika ya cancanci rike mukamin.

Tare da alkalin alkalan akwai wadansu masu shari’a da suka taya shi karbar bakuncin wannan kwamitin. Wadannan alkalan kuwa su ne, Jastis Sylvester Ngwuta, Mary Odili da Amiru Sanusi.

https://www.vanguardngr.com/2019/10/ive-zero-tolerance-for-corruption-forward-petition-against-erring-judges-%E2%80%95cjn/?utm_source=dlvr.it&utm_medium=twitter

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel