Da duminsa: Buhari da Jonathan sun shiga ganawar sirri a Aso Rock

Da duminsa: Buhari da Jonathan sun shiga ganawar sirri a Aso Rock

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, a fadar gwamnatin tarayya, Aso Rock, da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Buhari da Jonatahn sun shiga wata ganawa ta sirri da misalin karfe 3:00 na rana, jim kadan bayan isar tsohon shugaban kasa, Jonathan, fadar shugaban kasa.

Jonathan ya isa farfajiyar fadar shugaban kasa da misalin karfe 2:58 na ranar Alhamis.

Wannan shine karo na farko da tsohon shugaba Jonathan ya ziyarci fadar shugaban kasa Buhari tun bayan sake cin zabensa a karo na biyu.

Jonathan ya ziyarci fadar shugaban kasa a kalla sau biyu a zagaye na farko na mulkin shugaba Buhari.

DUBA WANNAN: An samu miliyan N135 a hannun janar din rundunar soji da ake tuhuma da karkatar da kudaden sojoji

Tun kafin hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da sakamakon zaben shekarar 2015, Jonathan ya kira Buhari ya taya shi murnar lashe zaben kujerar shugaban kasa, duk da shi Buharin ya kayar a wancan lokacin.

Buhari da Jonatahn na cikin ganawar sirri a daidai lokacin da Legit.ng ta wallafa wannan labari.

Da duminsa: Buhari da Jonathan sun shiga ganawar sirri a Aso Rock
Buhari da Jonathan a Aso Rock
Asali: Twitter

Da duminsa: Buhari da Jonathan sun shiga ganawar sirri a Aso Rock
Buhari da Jonathan suna gaisawa a Aso Rock
Asali: Twitter

Da duminsa: Buhari da Jonathan sun shiga ganawar sirri a Aso Rock
Buhari da Jonathan
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel