Assha: Wasu yan uwa 2 sun fille kan wani yaro domin siyar dashi kan N200,000

Assha: Wasu yan uwa 2 sun fille kan wani yaro domin siyar dashi kan N200,000

Wata babbar kotun Igbosere a Lagas ta tsare wasu yan uwa biyu Saheed Obadimeji da Ayodeji Obadimeji, a gidan yari a ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoba, bisa zargin fille wa wani matashin yaro kai.

An tattaro cewa yan uwan biyu sun fille kan yaron ne da niyan siyar dashi akan kudi naira 200,000.

Saheed dan shekara 19 da Ayodeji dan shekara 20, wadanda ke zama a yankin Ibeju-Lekki da ke Lagas, na fuskantar shari’a akan tuhume-tuhume biyu na hada kai wajen aikata kisan kai da kuma kisan kai.

Sai dai kuma sun ki amsa laifin tuhume-tuhumen da ake masu.

Mai gabatar da kara da jihar Lagas, Mista Tunde Sunmonu ya fada ma kotu cewa wadanda ake karan da wasu sun aikata laifin a ranar 27 ga watan Nuwamba, 2018 da misalin karfe 8:30 na rana a wani ginin kango a garin Sapati, Ibeju-Lekki, Lagas.

Yace masu laifin sun ja wani Joseph Makinde gefe, sannan suka yaudare shi zuwa kangon inda suka kashe shi.

KU KARANTA KUMA: Babban magana: EFCC ta kama dan damfara a fadar shugaban kasa

Yace wadanda ake karan sun kuma yanka kan matashin domin su siyar dashi akan N200,000.

Sanmonu yace laifin yayi karo da sashi na 223 da 233 na dokar jihar Lagas, 2015.

Don haka Justis Adedayo Akintoye, ya tsare su a gidan yari sannan y adage shari’an zuwa ranar 18 da 19 ga watan Nuwamba don cigaba da shari’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel