Sanata Okorocha ya samu Takwara bayan ya nemi a rage ‘Yan Majalisa

Sanata Okorocha ya samu Takwara bayan ya nemi a rage ‘Yan Majalisa

A Ranar Laraba, 9 ga Oktoba, Kungiyar hadakar jam’iyyun siyasar Najeriya ta CNPP ta fito ta na mai na’am da kiran da Sanata Rochas Okorocha ya yi na cewa akwai bukatar rage ‘yan majalisa.

CNPP wanda lema ce ta duk jam’iyyun kasar nan ta kuma yi magana a game da wani sabon kudiri da ake shirin kawowa na shigo da harajin sadawar a madadin kara harajin kayan masarufi.

A cewar CNPP, ba zai zama matsin lamba a kan Talakawa idan aka shigo salon harajin salula inda za a rika tatsar masu yin waya ko kuma hawan shafukan yanar gizo ta salula kamar karin VAT va.

CNPP ta bakin Willy Ezugwu, take cewa: “A wurinmu, kudirin da ke neman a fara karbar haraji a kan sakonni na SMS da MMS da kuma hawa yanar gizo da kallon talabiji zai zo da dan sauki.”

KU KARANTA: Ana neman soke rajistar tara-gutsan Jam’iyyu fiye da 80 a Majalisa

Mista Willy Ezugwu, wanda shi ne Sakataren kungiyar ya kara da cewa: “Tasirin da wannan haraji zai yi wa mutane ba zai kai karin harajin VAT na kashi 7.5% da gwamnati ta ke shirin yi ba.”

A game da maganar Okorocha kan ‘yan majalisa, tsohon gwamnan ya fadi gaskiya da yace Sanata guda a kowace jiha zai iya yin aikin da ‘yan majalisu har uku su ke yi a majalisar dattawa.”

“Don haka mu na kira ga Sanatan ya yi maza ya kawo kudirin da zai shafe dokokin tsarin mulkin Najeriya domin a yi wannan saboda gwamnati ta adana kudi ta yi wasu ayyukan.” Inji Ezugwu.

Tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha mai wakiltar Yammacin jihar yana ganin idan aka rage kujerun majalisa, za a samu rarar kudin da za a yi wa Talakawan Najeriya wasu ayyukan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel