An samu miliyan N135 a hannun janar din rundunar soji da ake tuhuma da karkatar da kudaden sojoji

An samu miliyan N135 a hannun janar din rundunar soji da ake tuhuma da karkatar da kudaden sojoji

An samu wasu kudi da yawansu ya kai miliyan N135 a hannun Manjo Janar Hakeem Otiki, babban soja da ake tuhuma da sata tare da karkatar da kudin rundunar soji.

Babban sojan, wanda yanzu ake tuhuma a gaban wata kotun rundunar soji ta musamman, ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Janar Otiki na cigaba da fafutikar neman kotun ta bashi dama ya fita zuwa birnin Florida na kasar Amurka domin a duba lafiyarsa.

Kazalika, babban sojan ya roki kotun ta umarci hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta bude asusunsa na ajiyar kudi da aka garkame tare da hana shi taba ko sisi a ciki.

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar soji ta aika kusan miliyan N160 zuwa ofishin rundunar dakarun soji da ke jihar Sokoto domin walwalar jami'anta a lokacin da janar Otiki ke shugabantar rundunar sojojin yankin.

DUBA WANNAN: Sabuwar doka: Za a iya daure mace na tsawon shekaru biyu a kan hana miji hakkin kwanciya - 'Yan sanda sun gargadi matan aure

Amma kudin, 100,000,000 da $86,000, sun yi batan dabo a hanyar Sokoto zuwa Kaduna bayan Janar Otiki ya umarci wasu sojoji su raka wani mutum, Alhaji Abo, daga Sokoto zuwa Kaduna tare da adadin kudin.

Sojojin da Janar Otiki ya umarci su raka Alhaji Abo sun hada baki tare da yi masa fashin kudin, 100,000,000 da $86,000, da Janar Otiki ya bashi a tsakanin Funtua zuwa Zaria.

Sojojin sun shiga jeji da Abo da abokinsa tare da kwace dukkan kudaden da kuma wayoyinsu na hannu.

Duk da bayanai sun nuna cewa za a kai kudin jihar Kaduna ne domin sayen kayan karau na cikin gida, binciken jami'an tsaro ya gano cewa akwai wata maganar a kasa bayan hakan, lamarin da yasa aka kama Janar Otiki tare da canja sabon kwamanda a rundunar sojojin da yake jagoranta.

Yanzu haka masu binciken Janar Otiki da wasu shaidu da aka gabatar a kansa, sun nuna cewa an samu nasarar kwace miliya N135 daga hannunsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel