Abubuwan da yakamata ku sani game da 'yar jaridar da ta bankado asirin malaman jami'a

Abubuwan da yakamata ku sani game da 'yar jaridar da ta bankado asirin malaman jami'a

- Lalata da malaman jami'a ke yi da dalibai mata ya zama ruwan dare a jami'o'inmu

- Akwai yuwuwar cewa, abinda ya faru da 'yar jaridar ne ya bata kwarin guiwar binciken da tayi

- Ta bar karatun likitanci a jami'ar najeriya dake Nsukka sakamakon cin zarafinta da aka yi yunkurin yi

Kiki Mordi 'yar jarida ce mai aiki da BBC wacce ta bankado asirin batagarin malaman jami'a.

Ta nadi bidiyoonsu don kafa kwakkwarar hujja akan cin zarafi tare da lalata da dalibai mata da suke yi a jami'o'i.

Mutane da yawa sun jinjina mata akan fallasar da tayi ga malamai masu mummunan halin neman dalibansu da lalata a jami'o'in Afirka ta kudu.

KU KARANTA: Wani malamin jami'a yace bidiyon fallassar da BBC ta yi kirkirarre ne

Ga abubuwan da yakamata ku sani game da ita:

1. 'Yar jaridar ta cika shekaru 28 a duniya ne a watan Augusta da ya gabata.

2. Asalinta 'yar jihar Rivers ce ta Najeriya.

3. Itace shugabar masu shirin gidan rediyon 'Women Radio FM 9.17'.

4. 'Yar fim ce, mai gabatarwa kuma marubuciya.

5. Ta bar karatun likitanci daga jami'ar Najeriya da ke Nsukka saboda cin zarafin neman yin lalata da ita.

6. Tana zama ne a Turai.

7. Ta yi bincikenta na karshe ne wanda ya bankado asirin malaman jami'ar jihar Legas da jami'ar Ghana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel