Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da kwamitin da ke bai wa Shugaban kasa shawara game da cin-hanci da rashawa ranar Alhamis a fadar Villa.
Kamfanin dillacin labaran Najeriya, NAN Ya tattaro mana cewa an kafa wannan kwamitin ne a shekarar 2015. Kuma wannan gwamnatin ta Buhari ta kafa shi ne domin kawar da cin-hanci da rashawa a kasar nan.
KU KARANTA:Zaben Kogi: Mahmoud Yakubu ya isa Kogi domin ganawa da masu ruwa da tsaki game da zaben
Daga cikin ayyukan da kwamitin ke yi akwai, kwaskwarima ga dokokin yaki da cin-hanci, bayar da shawara game da yadda za a yaki cin-hanci da kuma kaddamar da hanyoyin hukunci ta amfani da karfin shari’a.
Idan baku manta ba a ranar 1 ga watan Oktoba, Shugaba Buhari ya sake jaddadawa a cikin jawabinsa irin kudurin da yake da shi na ganin ya kawo karshen cin-hanci a kasar nan.
Ya kuma yi alkawarin gudanar da sahihiyar gwamnati mai nagarta ta yadda ko wace ma’aikata za ta tsaya iyakacin bakin aikinta.
Buhari ya ce: “Ma’aikatar shari’a, hukumar yaki da cin-hanci da laifuka ire-irensa ta ICPC da kuma hukumar yaki da cin-hanci da kuma yiwa tattalin arziki zagon kasa EFCC za su cigaba da duba wannan al’amari.”
A wani labarin kuwa zaku ji cewa, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya isa birnin Lokoja domin ganawa da ‘yan takarar gwamnan jihar Kogi a zaben da za ayi cikin wata mai zuwa.
https://leadership.ng/2019/10/10/pmb-meets-members-of-advisory-cttee-against-corruption/
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa