Zaben Kogi: Mahmoud Yakubu ya isa Kogi domin ganawa da masu ruwa da tsaki game da zaben

Zaben Kogi: Mahmoud Yakubu ya isa Kogi domin ganawa da masu ruwa da tsaki game da zaben

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya isa Lokoja babban birnin jihar Kogi domin ganawa da masu ruwa da tsaki a kan zaben gwamnan jihar dake tafe ranar 16 ga watan Nuwamba.

Wadanda suka halarci ganawar sun hada da dan takarar APC, Gwamna Yahaya Bello da kuma abokin takararsa na PDP, Engr. Musa Wada da sauran ‘yan takarar jam’iyyun siyasa daba-daban.

KU KARANTA:Buhari ya gana da kwamitin shawara game da cin-hanci da rashawa a Villa

Ana gudanar da ganawar ne a otel Idrinana dake Lokoja. A cikin jawabinsa na maraba, Mahmoud ya ce wannan zaman na daga cikin kokarin hukumar INEC na ganin an gudanar da zaben cikin lumana da kwanciyar hankali.

Haka zalika, hukumar zaben ta tanadi ma’aikata 26,000 a matsayin sojojin haya wadanda za su gudanar da ayyukan zabe a jihohin Bayelsa da Kogi ranar 16 ga Nuwamba.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu ya fadi wannan maganar ne a lokacin da ya ziyarci ofishin INEC na Koton-karfe a ranar Alhamis.

“Ina mai sanar da ku cewa zaben game da Kogi da Bayelsa mun tanadi sojojin haya 26,000 wadanda za suyi aikin bayan mun basu takardun aiki a ranar zabe.

“Kunshe a cikin takardar akwai adadin kudin alawus da za a ba ma’aikatan bayan an kammala zaben, tare kuma yadda ake aikin da kuma gudanar da korafi abin ya tafi ba daidai.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel