Sanatoci sun soma muhawara a kan kundin kasafin kudin 2020

Sanatoci sun soma muhawara a kan kundin kasafin kudin 2020

Wasu daga cikin Sanatoci sun bankado abubuwan da su ke yi wa kallon kura-kurai a cikin kasafin kudin shekara mai zuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a farkon makon nan.

Daily Sun ta rahoto cewa an fara tafka muhawara a majalisar dattawa game da kasafin Najeriyar na shekara mai zuwa inda Sanatocin jam’iyyar APC da PDP duk su ke tofa albarkacin bakunansu.

Shugaban masu rinjaye a majalisar, Yahaya Abdullahi, ya koka a game da karancin abin da aka ware domin gina abubuwan more rayuwa idan aka yi la’akari da karfin tattalin arzikin kasar.

A lokacin da majalisar ta ke duba batun bashin makudan kudin da gwamnati za ta ci, Sanata Yahaya Abdullahi na APC ya ke cewa Naira tiriliyan 2.46 domin yin aikace-aikace ya yi kadan.

Wasu manyan ‘yan majalisar sun kuma soki gaba daya lamirin kasafin na badi inda su ke ganin cewa an shirya lissafin kudin na 2020 ne kurum a kan kanzon kurege domin ba za a kai labari ba.

KU KARANTA: Majalisa ta yi magana a kan wata matsala da ta addabi Najeriya

Abdullahi ya nemi gwamnatin tarayya ta dage da tatsan kudi wajen hukumomin da aka ba alhakin karbar haraji da samun kudin-shiga. Sanatan ya kuma nemi a jawo masu hannun-jari.

Bayan batun karkato da hankalin ‘yan kasuwa, Sanata Abdullahi ya ba gwamnati shawara ta kara kokari wajen saukaka kasuwanci da yaki da cin hanci tare da samar da ayyukan yi ga mutane.

Sanatocin su na ganin cewa idan aka yi la’akari da kudin da Najeriya ta ke neman aro a 2020, abin da za a kashe wajen gina hanyoyi da layin dogo da sauran abubuwan more rayuwa sun yi kadan.

A na sa jawabin, shugaban marasa rinjaye, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya caccaki kundin kasafin inda yace gwamnatin tarayya ta gaza wajen hasashen motsawar tattalin arzikin da ta yi na badi.

Enyinnaya Abaribe ya ji dadin yadda wani Takwaransa ya kushe kasafin. Sanatan na Abia yace gwamnatin Buhari ta ci buri sosai a kan iska wanda yake ganin zai yi wahala kasar ta kai ga ci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel