Mun san wajen da dalibai da malamai da aka sace suke – Yan sanda

Mun san wajen da dalibai da malamai da aka sace suke – Yan sanda

Rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna a ranar Laraba ta bayyana cewa, ta shiga tattaunawa da yan bindigan da suka sace dalibai mata shida, malamai biyu da aka sace daga makarantar su a ranar 3 ga watan Octoba.

Rundunar har ila yau tace ta kama masu laifi 50 wadanda ke da hannu wajen aikata laifuffuka daban-daban a fadin jihar da kuma kwato bindigogi 27.

Kwamishinan yan sandan jihar, Mista Ali Janga ne ya fadi haka a wani taron manema labarai a Kaduna.

Janga ya bayyana cewa yan sandan sun nemi tattaunawa da yan fashin gudun kada rayukan daliban ya kasance cikin hatsari.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta tuna a baya cewa an sace mata shida da ma’aikata biyu a kwalejin Engravers a daren ranar Alhamis.

Janga ya bayyana cewa daga cikin masu laifi 50 da aka kama harda yan bindigan da suka yi garkuwa da wani babban malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Algarkawi da dan majalisan dokokin jihar, Suleiman Dabo.

KU KARANTA KUMA:

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare na gwamnati wato 'Government Technical Secondary School' dake kauyen Maraban Kajuru, a karamar hukumar Kajuru dake jihar Kaduna, inda suka sace shugaban makarantar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel